Michael ya ji rauni a idon sawun sa wanda ya sa ba zai buga gasar AFCON 2021 da kuma mafi yawan lokutan kakar 2021-2022 ba.
Dan wasan mai shekaru 22 ya fuskanci mummunan rauni a wasan da Bologna ta yi 1-1 da Udinese a ranar 17 ga Oktoba 2021.
An yi wa Kingsley tiyata nan da nan bayan ya ji rauni kuma yanzu ya koma atisaye.
Kafin rauninsa, Michael ya buga wasanni biyu a kungiyar ta Seria A yayin da duka biyun suka zo a madadin.
Da yake mayar da martani game da dawowar sa, dan wasan ya ce ba zai iya jira ya dawo filin wasa ba.
“Ranar farko a filin wasa bayan watanni 4, a wurin Allah komai mai yiwuwa ne. Naji dadi na saka takalmin ƙwallon ƙafata, ba zan iya jira in fara da ƙungiyar ba🙏